A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, daga Ofishin Sheikh Zakzaky (H) Jagoran Harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya gudanar da taron zaman cika kwanaki bakwai da shahadar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei wanda kuma yayi daida da daren sha tara ga Ramadan, daren da la'ananne Ibn Muljam ya sari Imam Ali (AS).
Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana cewa: "Baya ga jajantawa da muka yi ta yi, mun ga cewa ya kamata mu zauna a daidai wannan lokaci, wanda ya zama kuma yau 18 ga watan Ramadan, a yayin da muke jajen 7 din Shahadar Sayyid Khamenei, a lokaci guda kuma lokacin jajen Shahadar Amirulmumin (AS) ne, domin daren da ke gabanmu daren 19 ne ga watan Ramadan wanda a safiyar wannan dare ne al-la'in Ibn Muljam ya sare shi da takobi a masallaci."
Jagora bayan da ya kawo tarihin rayuwar Sayyid Khamenei da darussa daga rayuwarsa, ya kuma jaddada irin rashin da aka yi inda ya ce: “Mun yi babban rashi. Mun san mun yi rashin wani babban gwarzo wanda ya tsaya tamkar Marigayi Al-Imam Khomaini (QS), wanda kuma mun san wannan baiwa ne daga Allah Ta'ala.”
Ya ci gaba da cewa, "a lokaci guda kuma, mun san dama lazim ne wani lokaci za a tafi. To Allah Ta'ala Ya kaddara tafiyar (Sayyid Khamenei) ta hanyar Shahada ne a wata mai tsarki kamar lokacin Shahadar kakansa Amirulmumin (AS).”
Da yake tsokaci akan shirin makiya, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya jaddada musu cewa, batun suce za su kawar da Jamhuriyar Musulunc| ta Iran, suna mafarki ne, domin kuwa suna fada da Allah Ta'ala ne. Yace: “(Na'am) za ku yi barna. Barnar da za ku yi, zai zama mu a wurinmu Shahada ne, abinda za a sadaukar kenan. Amma nasara daga wajen Allah, to dama Aqiba aka yi mana alkawari. Farko ana iya jin jiki, amma Aqiba alkawarin da aka mana kenan. Kuma fatanmu na bayyanar Qa'im (AS) na nan, muna ganin kamar lokaci ake jira.”
Jagora (H) ya tunatar da 'yan uwa muhimmancin raya daren da ke gabanmu na 19 ga watan Ramadan da ibadodi, a matsayinsa na daya daga cikin Layalil Qadr. Yace: "A safiyar wannan daren ne aka sari Amirulmumin, don haka ma ana la'antan makasan Amirulmumin da cewa Allahummal'an qatalata Amirulmumin har sau dubu.”
Ya kara da cewa: "A daidai wannan lokaci, a hada da la'anta ga makasan Sayyid Khamenei da cewa Allahummal'an Qalatala Sayyid Khamenei.”
Ya cigaba da cewa:" La'antan makasan Amirulmumin a lokaci guda la'antan makasan yayansa ne, kuma Sayyid Khamenei yana ciki. Saboda haka daidai wannan lokaci ne da za a kara kaimi da ibadodi a daren 19 da daren 21 da daren 23, wanda mukan raya su gabadaya da salloli, da addu'o'i.”
Jagora (H) ya bayyana babban gudummawar da za mu bayar a wannan halin shi ne addu'a. “Mu dage, mu yi ta addu'a dare da rana, musamman a wannan wata mai alfarma.”
Ra'ayinka